Quran Offline | Mallam Jaafar

Quran Offline | Mallam Jaafar

Qira'ar Karatun Al-Qur'ani

开发者: Abdulkarim Nasir

中国
APP ID 复制
1659291402
分类
价格
USD1.99
内购
0个评分
音乐(付费)
昨日下载量
最近更新
2022-12-15
最早发布
2022-12-14
版本统计
  • 742天11小时

    最新版本上线距今

  • 0

    近1年版本更新次数

  • 2022-12-14

    全球最早版本上线日期

版本记录
显示信息
日期
  • 全部
每页显示条数
  • 请选择
  • 版本: 1.1

    版本更新日期

    2022-12-15

    Quran Offline | Mallam Jaafar

    Quran Offline | Mallam Jaafar

    Qira'ar Karatun Al-Qur'ani

    更新日志

    暂无更新日志数据

    视频/截图

    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图
    Quran Offline | Mallam Jaafar App 截图

    应用描述

    Ku sauke wannan manhajja ta karatun alqurani domin sauraron Qira'ar Malam Jafar. Yana aiki ba tare da internet ba. Wannan manhajja kyautace kuma babu talla cikinta.

    Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an) ko kuma Alkur'ani mai girma kamar yadda musulmi suka fada, littafi ne mai tsarki wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga annabin musulunci Muhammad (SAW). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin akidar Musulunci, Kur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Muhammadu, yana tabbatar da cewa Muhammadu Annabi ne na gaskiya.

    Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na dan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.

    Application features:
    1. Full Quran mp3 offline 114 Quran Surahs
    2. Search Surah by Surah-name or Surah number
    3. Makki surahs indicated by masjid al-haram image i.e Holy Kaabah
    4. Madani surahs indicated by masjid an-nabawi image (The Prophet (s.a.w) Holy Mosque in Madinah)
    5. Ability to mark Surah as favourite.
    6. Favourites list view provided. Remove or listen to favourited Surah
    7. You can share the app with your family and/or friends
    8. Surah info in English, Arabic and Hausa languages.
    9.Beautiful Islam gallery featuring al-Kaabah, masjid an nabawi, Quran and more. Add or remove the provided islamic photos
    10. Play, pause, next and previous controls. You can also shuffle or repeat a Surah
    11. Quran surah names in English and Arabic
    12. The number of verses of each Surah is indicated
    13. Mute or unmute Quran Surah while playing.
    14. Ability to read the Quran in mush style while listening
    15. Play Malam Jafar Qira'a in background
    16. Free without Ads

    Tarihin shigowar Musulunci a Kasar Hausa:
    A game da kasar Hausa, tarihi ya nuna mana ba a shigo mana da musulunci ta hanyar karfi ba. A’a musulunci ya shigo mana ne ta hanyoyin fataucin kasuwanci da kuma matafiya na sa-kai don neman tarihin kasa da da’awa ta wa’azi da kuma hanyar kaurace-kaurace na kabilu da al’ummu daga wuri zuwa wuri kamar yadda ya gabata.

    ‘Yan kasuwa su ne suka fara shigowa da musulunci kasar nan, amma ta hanyar daidaikun mutane ne. Wasu ma suna ganin tun a farkon karni na Hijirar Manzon Allah (S.A.W) musulunci ya fara saduwa da kasar Hausa ta gefen Katsina zuwa Kano, inda matafiya na kasuwanci suke bi daga wasu kasashe na Larabawa. Su ne kuma suka shigo mana da musulunci ta wannan hanyar zuwa arewacin Nijeriya.

    Sannan hanya ta biyu ita ce ta wurin matafiya don rubuta tarihin kasa kamar su Ibn Khaldun da masu wa’azi kamar su Al-Maghili. Ta wannan fuskar sun fi mai da hankalinsu ta saduwa da sarakuna da mahukunta da malamai. A wannan hanyar ta biyu sun zo ne daga baya, kuma sun samu kasar Hausa cike take da mabiya addinin musulunci musamman ma talakawa. Watau dai a takaice talakawa sun fara karbar musulunci a kasar Hausa kafin sarakunansu su karbe shi. Misali, sarkin Katsina Korau (1320-1353) shi ne ya fara karbar addinin musulunci, sai sarkin Kano Yaji (1349-1385) wanda Wangarawa suka zo a lokacinsa, suka shigar da shi addinin musulunci. Sai sarkin Zazzau wanda ya musulunta na farko cikin sarakunanta shi ne Muhammadu Rabo. A masarautar Zamfara kuwa musulunci ya fara shigowa ne shekara ta 1640 A.D. Amma an ce kasar Zamfara ta karbi musulunci kafin 1640 A.D shi ne ingantacce. Haka dai sarakunan suka rika musulunta suna karfafa Hakimai da Dagatai nasu a cikin musulunci da masu unguwanninsu har zuwa ga talakawa.
    Misali, a zamfara akwai wasu malamai wadanda ake kira malamai na ‘Yan Doto. Su wadannan malamai suna kasar Zamfara tun shekaru aru-aru kafin bayyanar Shehu Usman dan Fodiyo. Wadannan malamai su ne ake kyautata zaton cewa su suka rubuta wasu shahararrun littattafai ‘yan kanana cikin Ilmin Fiqhu da Tauhidi da sauransu. Kamar littafin Qawa’idi da Rashada da Ma’anar La’ilaha illallahu Muhammadur- Rasulullahi da makamantansu.